Luke 12

Faɗakarwa da Ƙarfafawa

1Ana nan saʼad da taron dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, Yesu fara yin magana, da farko da almajiransa, ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, munafunci. 2Ba abin da yake rufe da ba za a fallasa ba, ko kuma abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. 3Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan na ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna.

4“Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. 5Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. 6Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. 7Hakika, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.

8“Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban malaʼikun Allah. 9Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban malaʼikun Allah.

10“Kuma duk wanda ya faɗi kalmar zagi a kan Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya saɓa wa Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.

11“Saʼad da an kai ku a gaban majamiʼu, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa, 12gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”

Misali na Wawa Mai Arziki

13Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗanʼuwana ya raba gādon da ni.”

14Yesu ya amsa masa, ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?” 15Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”

16Sai ya gaya musu wannan misali, ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17Ya yi tunani a ransa, ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’

18“Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki.’ 19Ni kuma zan ce wa raina, ‘Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.’

20“Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a bidi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’

21“Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”

Kada Ku Damu

22Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa. 23Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24Ku dubi hankaki. Ba sukan yi shuki ko girbi ba, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa! 25Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, na iya ƙara ko saʼa ɗaya ga rayuwarsa? 26Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran?

27“Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba. 28In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, saʼan nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. 30Gama duniya ta masu bautar gumaka, da ba ta san Allah ba, tana faman neman dukan irin waɗannan abubuwa. Amma Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu. 31Amma ku bidi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.

32“Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin. 33Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakunkuna da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za ta kare ba a sama, inda ko ɓarawo ba zai yi kusa ba, ko kuma asu ba za su iya su lalatar ba. 34Gama inda dukiyarku take, a nan ne zuciyarku ma take.

Zama a Faɗake

35“Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci, 36kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan. 37Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, saʼan nan ya yi musu hidimar abinci. 38Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a cikin saʼa ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne. 39Amma ku fahimci wannan: Da maigida ya san saʼar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba. 40Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a saʼar da ba ku yi tsammani ba.”

41Bitrus ya yi tambaya, ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa ga kowa da kowa ne?”

42Ubangiji ya amsa, ya ce, “To wane ne manaja mai aminci da hikima, wanda maigida ya ba shi riƙon bayinsa, domin ya ba su abincinsu a daidai lokaci? 43Zai zama da albarka ga bawan nan wanda maigidan ya dawo, ya same shi yana yin haka. 44Gaskiya nake gaya muku, maigidan zai ba shi riƙon dukan dukiyarsa. 45Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa, ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ saʼan nan ya fara dukan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa. 46Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a saʼar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya.

47“Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka. 48Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi.

Ba Salama ba Sai dai Rabuwa

49“Na zo ne domin in kawo wuta a duniya. Ina so da ta riga ta kunnu! 50Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta! 51Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? Aʼa! Ina gaya muku, rabuwa ne. 52Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun. 53Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”

Fahimtar Lokatai

54Ya ce wa taron, “Saʼad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi. 55Saʼad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi. 56Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba?

57“Don me ba ku iya auna wa kanku, abin da yake daidai ba? 58Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku. 59Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.”

Copyright information for HauSRK